Fishi sifface daga cikin siffar dan Adam wadda Allah ya halicci dan Adam akansa,kuma yayi masa umarnin yayi kokarin rage fishi ko nisantarsa abisa harshen Annabi SAW Wasu masana yanayin dan adam suna cewa: _"Fishi wani zafine yake faruwa acikin zuciyar dan Adam sai ya dumama jini da zuciya take har bawa sai hakan ya chanza dukkan yanayi dan Adam,wasu kuma suna cewa;Shaidhan ne yake rura wata wuta mai zafi azuciyar dan adam sai hakan ya chanza yanayinsa shiyasa Annabi SAW yayi umarni ga mai fishi ya nemi tsarin Allah daga shaidhan"_ Allah ne mafi sani. Fishi kala biyune akwai: 1-Fishi abin yabo Wato fishi na wajibi *"Shine fishi dan an daba addinin Allah ko an taba wata martaba ko koyarwa ta Allah da manzonsa,wannan shine fishin da Annabi SAW yake idan an taba addinin Allah*. Nana A'isha R.A tana cewa: "Da daya Annabi SAW bai taba yin fishiba ko daukar fansaba dan an taba wani abu nasaba sai dan yana yin fishi idan an taba addinin Allah". @Bukhari. 2-Fishi abin zargi Wato fishin da yin sa yakan zama haramun ko makaruhe. *"Shine yin fishi dan an taba matsayi naka ko martatarka ko wani daga cikin kusa da kai,wato aiyi fishin ne dan kare martabar kai ba kare addinin Allah da Manzonsa ba"*. *_FALALAR NISANTAR FISHI DAN AN TABA KA KO AN BATA MAKA RAI_* _1-Barin fishi yana jawowa mutum samun son Allah a gareshi_. Allah yana cewa: (الَّذِينَ يُنفِقُونَ فِي السَّرَّاءِ وَالضَّرَّاءِ وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ ۗ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ ) (Waɗanda suke ciyarwa a cikin sauƙi da tsanani kuma suke mãsu haɗiyẽwar fushi, kuma mãsu yãfe wa mutãne laifi. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa). @آل عمران (134) Aal-Imran _2-Nisantar fishi da barinsa wasiyyace daga cikin wasiyyoyin Manzon Allah SAW_ Wani mutum yacewa Manzon Allah s.a.w kayi min wasiyya sai yace: *(Kada kayi fishi)*Sai ya sake maimaitawa kayi mini wasiyya sai yace: *(Kada kayi fishi)*. @رواه البخاري. 3-Wani mutum ya cewa Annabi SAW ka bani labari da wadansu kalmomi wanda wanda zan rayu akansu amam kada ka yawaita min su,sai yace da shi: *(Ka nisanci fishi)* sai ya kara tambayarsa akan haka sai yace: *(Ka nisanci fishi)*. @السلسلة الصحيحة (884) . _4-Ka nisanci fishi zaka shiga Aljanna_. Wani mutum yacewa Manzon Allah SAW SAW kayi min nuni zuwa ga wani aiki da zai shigar dani aljanna sai yace: *(Kada kayi fishi zaka shiga aljanna)*. @صحيح اﻷدب المفرد (2749 _5-Ka nisanci fishi kana da yan matan Hurul'in_. Manzon Allah SAW yana cewa: *(Dukkan wanda ya hadiye fishi alhalin yana da damar daukar fansa,Allah madaukakin sarki zai kirasa a gobe alqiyama a tsakiyar mutane ya bashi damar ya zabi yan matan Hurul'in yadda yaga dama)*. @صحيح الترغيب (2753). Amma yin fishi dan Allah saboda an taba addinin Allah ko martabar Allah da Manzonsa SAW wannan fishi wajibine. Saboda Hadisin Nana A'isha R.A tana cewa: *(Annabi SAW bai taba yin fishi ba ko daukar fansa ba ko sau daya ba sai idan an taba Alfarmar Allah)*. @أخرجه البخاري ومسلم. Allah ne mafi sani.